Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Gwamnonin Najeriya Ta Goyi Bayan Amfani Da Riga-kafin AstraZeneca


Samfurin allurar riga-kafin AstraZeneca
Samfurin allurar riga-kafin AstraZeneca

Membobin Kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, sun goyi bayan ci gaba da rabawa da kuma yin allurar AstraZeneca a duk fadin kasar.

Sun tabbatar da fa'idar allurar rigakafin, su na masu jaddada cewa babu wata illa da aka samu daga wadanda suka karbi allurar ya zuwa yanzu a Najeriya.

Damuwa game da amfani da allurar AstraZeneca, da aka dakatar a wasu ƙasashe, na cikin ajandar tattaunawar taron NGF da aka gudanar a ranar Laraba.

Taron, wanda shugaban NGF kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya jagoranta, ya samu takaitaccen bayani game da matsayin allurar rigakafin daga kungiyar COVID-19 Technical Advisory Group, ko kuma CTAG a takaice, karkashin jagorancin shahararren masanin ilmin likitanci, Farfesa Oyewale Tomori.

A bayanin da ta gabatar, CTAG ta ba da shawarar cewa Najeriya ta ci gaba da yi wa duk wadanda suka cancanta allurar rigakafin ta AstraZeneca, daidai da sabbin shawarwarin Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

Amma sun yi kira ga mutane da su kai rahoton duk wata mummunar illa da ta auku bayan shan allurar rigakafin. A nasa jawabin, Fayemi ya taya takwarorin aikinsa murna bisa yarda da yin allurar tare da ayyana cewa kawo yanzu, allurar rigakafin ba ta nuna alamun illa ba kamar yadda aka ruwaito.

XS
SM
MD
LG