Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Saka Dokar Zama a Gida a Bahamas


Frai Ministan Bahamas, Hubert Minnis
Frai Ministan Bahamas, Hubert Minnis

A yau Talata ake sake rufe kasar Bahamas na tsawon makwanni 2 sanadiyyar sake barkewa da cutar coronavirus ta yi.

Firai ministan kasar Dr. Hubert Minnis ne ya sanar a jawabin da yayi ta kafar talabijin da daren jiya Litinin, in da ya fadi cewa an dau wannan matakin ne bisa shawarar masana harkar lafiya.

Minnis ya ce jami’ai za su yi nazarin ingancin kullen bayan makwanni 2 sannan a dau matakin sassautawa tare da hadin gwiwar mutanen kasar.

Ya kuma cewa za a ci tarar wadanda aka same su da cutar kuma suka karya dokar killacesu da akayi.

An kaiyade fita domin sayen kayan abinci ko ruwa ko magani ga ranakun Litimin, Talata da Laraba ne kawai daga karfe 7am zuwa 5pm na yamma ga al’ummar gari amma jami’ai da ake bukatar aikinsu na da Karin ranar Asabar da zasu iya fita.

Minnis yace akwai bukatar ‘yan kasar da mazauna kasar su hada kai domin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Mafi yawan masu dauke da COVID-19 an gano su ne a watan da ya gabata, wanda a halin yanzu an samu mutum 14 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG