A wani mataki na takaita yaduwar cutar coronavirus, gwamnatin Najeriya ta hana jami’an ta zuwa kasashen waje kamar su China, Amurka, Birtaniya, Japan, Switzerland da Netherland. Sauran kasashen sune Iran, Norway, Faransa, Koriya ta kudu, Jamus, Italiya da Spain.
To amma bisa ga dukkan alamu, wannan matakin bai gamsar da mafi yawan kwararru a bangaren kiyon lafiya na kasar ba.
Babban daraktan cibiyar dake kula da ayyuka da bincike kan cututtuka masu yaduwa na jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Isa Sadik Abubakar, ya ce, hanyoyin da za a bi domin hana yaduwar cutar sune, hana taron mutane da yawa da kuma hana mutanen da watakila sun riga sun kamu da cutar shiga kasar.
Ya kara da cewa dole ne sai an dauki matakan rufe duk iyakokin shigowar kasar, kamar filayen jirgin sama, jiragen ruwa da hanyoyin mota.
Dr. Nasiru Sani Gwarzo, kwararren likita ne a Najeriya, ya ce, duk kasar da ta kai mataki na uku da ake kira "Community transmission" wato yaduwar cutar cikin al’umma, to bai kamata a bar ‘yan wannan kasar su shigo cikin Najeriya ba. Ya kuma ce, matakin rufe iyakoki shine daidai.
Shi ma Dr. Faruk BB Faruk, babban malami a jami’ar Abuja, ya ce Najeriya ba ta makara ba wajen dakile yaduwar cutar. Kasashe kamar Ghana da Chadi, duk sun takaita masu shigowa kasarsu saboda hana yaduwar cutar a cewarsa.
A nasa bangaren, Sa’ad Usman, mai sharhi akan al’amurran yau da kullum, ya ce idan an ce za a rufe iyakokin Najeriya, to tabas matakin zai shafi rayukan al’umma.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum