Wannan ya biyo bayan kalaman da wani mutum yayi, wanda yace shi sojan Najeriya ne, kuma har ma yayi karin haske dangane da yaki da kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram.
Rafsanjani ya kara da cewa cin hanci na daya daga cikin dalilan da yasa ake samun rashin nasara wajen kawar da ta’addanci.
Mr. Awwal ya kara da cewa "rahotanin dake fitowa, ba abin mamaki bane domin dama jama’a na hasashen haka, ganin yadda jami'an tsaron najeriya suka kasa shawo kan matsalar tsaro a Najeriya."
”Saboda akwai wadanda ake amfani da su a cikin jami’an tsaron ake kulla wannan cin hancin ake ta amfani dasu don su sami riba ko don su sami kudi ko kuma su sami wata bukata saboda tsaban sonkai da kuma rashin adalci ga jama’an kasa”, a cewar Mr. Rafsanjani.
Yace rashin adalci da kuma take hakkin bil adama ba zai sa a sami cigaba da zaman lafiya ba.