Da safiyar yau Laraba, Korea ta Arewa, ta harba wasu makamai masu linzami guda biyu da ke cin gajeran zango, a cewar dakarun Korea ta Kudu.
Wannan shi ne karo na biyu, da Pyongyang, ke gwajin makamin cikin mako guda, yayin da tattaunawa kan shirin nukiliyan nata ta cije.
Makaman masu linzamin, wadanda aka harba su, a kusa da gabashin birnin Wonsan mai tashar jiragen ruwa, sun yi tafiyar nisan kusan kilomita 250, a cewar shugaban gamayyar hafsoshin dakarun Korea ta Kudu.
Gwajin na zuwa ne kwanaki shida, bayan da Korea ta Arewa ta yi gwajin wani makami mai linzami nau’in ballistic, wanda aka ce, martani ne, ga shawarar da Korea ta Kudu ta yanke ta sayen makamai daga hannun Amurka, da kuma gudanar da rawar soji da ta yi da ita.
Facebook Forum