Birnin da cutar coranvirus ta fi muni a China, a karon farko ya kwashe tsawon wuni guda ba tare da samun rahoton wani ya kamu da cutar coronavirus ba, inda a yau Alhamis aka bayyana cewa babu mutum ko daya da ya kamu da cutar a jiya Laraba.
Garin Wuhan ya kwashe kusan watanni biyu a rufe, a yayin da hukumomi ke kokarin dakile yaduwar cutar, kuma a cikin 'yan makonnin nan adadin sabbin masu kamuwa da cutar ya ragu.
A wasu wuraren a China kuma, inda jami'an kiwon lafiya suka bada rahoton adadin mutune 34 da suka shiga kasar daga wasu wurare sun kamu da cutar a yau Alhamis, ana ci gaba da nuna damuwa akan yadda shigo da cutar daga wasu kasashe ke barazana ga ci gaban da kasar ta samu wajen yaki da cutar.
Kasar China ce cutar coronavirus ta fi shafa tun bayan bullarta a karshen watan Disamban bara, inda jimlar wadanda suka kamu da cutar ya kai kusan 81,000 da kuma mace-mace 3,200. Galibin wadanda suka kamu da cutar sun warke.
Facebook Forum