Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada ‘Yar Asalin Najeriya Kemi Badenoch Sakatariyar Harkokin Cinikayyar Kasa Da Kasa Ta Birtaniyya


Kemi Badenoch/Facebook
Kemi Badenoch/Facebook

Kemi Badenoch wadda ta nemi mukamin Firaiministan Birtaniyya, na fatan fara aiki a matsayin sakatariyar harkokin cinikayyar kasa da kasa don samar da ayyuka da ci gaban tattalin arziki.

WASHINGTON, DC - Sabuwar Firaiministar kasar Birtaniyya Liz Truss ta zabi 'yar majalisar dokoki, 'yar asalin Najeriya Kemi Badenoch ta zama mamba a majalisar ministocinta.

An nada Badenoch a matsayin sakatariyar harkokin cinikayyar kasa da kasa kuma shugabar hukumar kasuwancin kasar, a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin twitter sabuwar Firaiminstar.

Hakazalika, sanarwar ta bayyana sunayen sauran ministocin da za su yi aiki da Truss da sarauniyar Ingila Elizabeth ta amince da su.

Badenoch na daya daga cikin wadanda suka fafata a neman takarar mukamin Firaiminista da kuma shugabancin jam'iyyar Conservative ta masu ra’ayin mazan jiya.

Da take maida martani ta shafin twitter, Badenoch ta bayyana farin cikinta game da nadin da aka mata tare da fatan fara aiki don kawo ci gaba a fadin kasar.

XS
SM
MD
LG