A safiyar yau litinin, a makarantar CEG 11 da ke Yamai ministan kiwon lafiyar al’uma, Dr. Iliyasu Idi Mainassara, ya kaddamar da jarabawar cancantar aikin likitancin.
Dalibai 2,780 ne ke rubuta wannan jarabawa da ke ba da damar tantance wadanda suka lakanci ka’idodin aikin kula da marasa lafiya a asibitoci.
Dalibai sama da 300 ne aka hana shiga wannan jarabawar bayan da bincike ya gano suna dauke da takardun kammala karatu na bogi.
Dukkan wani yunkurin jin ta bakin shuagabanin makarantun da wannan mataki ya shafa ya cutura.
Amma ‘yan rajin kare hakkin bil’adama irin su Alhaji Salisu Amadu na kungiyar CCAC na mai bayyana takaici akan faruwar wannan al’amari da suka danganta da sakacin magabata.
Kungiyar lafiya ta kasashen Afrika ta Yamma da ake kira OAS ce ta umurci gwamnatocin kasashen wannan yanki su shirya irin wannan jarabawa a kowace shekara.
Dabarar yin hakan ita ce, a magance matsalolin da ke da nasaba da rashin sanin makamar aikin likita bisa la’akari da cewa a ‘yan shekarun nan ana ta samun yawaitar kafuwar makarantu masu zaman kansu da ke horar da jami’an kiwon lafiya.
Facebook Forum