Ana kyautata zaton 'yan adawa a Burtaniya za su gabatar da wata doka a yau Laraba, don sake jinkirta ficewa daga Tarayyar Turai don cimma sabuwar yarjejeniya kan sharuddan ficewar.
Firayim Ministan biritaniya, Boris Johnson, wanda ya yi alkawarin za’a aiwatar ficewar biritaniya daga tarayyar turai a ranar 31 ga Oktoba, ko akwai yarjejeniya ko babu, ya ce, matakin da majalisa ta dauka, ba wani zabi, face kiran a fara zabuka.
'Yan tawaye a majalisar sun sabawa doka bayan sun sami kuri'u 328 zuwa 301 a majalisar wakilai don karbe ragamar mulkin a kan yarjejeniyar ficewar ta Brexit. Wadanda ke adawa da yarjejeniyar ficewar ta Brexit sun ce, Johnson ya ci gaba ba tare da wata yarjejeniya ba, hakan zai iya haifar da matsala ga tattalin arzikin Birtaniyya.
‘Yan majalisar ‘yan tawayen sun hada da mambobi daga jam’iyyun adawa da kuma ‘yan jam’iyyar Johnson, masu ra’ayin mazan jiya.
Facebook Forum