Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben ‘Yan Majalisu Dokokin Kasar Togo


Zaben Kasar Togo
Zaben Kasar Togo

A ranar Litinin ne ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Togo bayan wani garambawul na kundin tsarin mulkin kasar, wanda ‘yan adawa ke cewa shi ne ya share fage ga shugaba Faure Gnassingbe na tsawaita mulkin iyalansa na tsawon shekaru da dama.

A kan karagar mulkin karamar kasa dake yammacin Afirka kusan shekaru 20, shugaba Gnassingbe ya gaji mahaifinsa Gnassingbe Eyadema, wanda ya yi mulki kusan shekaru arba'in.

Masu sukar lamiri sun ce za a tsawaita wa'adin mulkin daular siyasa a kan wannan karamar kasa ta yammacin Afirka ta hanyar yin garambawul.

Kawunan jama'a a titunan Lome babban birnin gabar teku sun banbanta kan zaben, matsayin shugaban Togo, da kuma wanda ya kamata ya mulki kasar.

A cewar wani mai sana’ar yin fenti a Togo Komlan Gato, “Mun gaji da ganin iyali guda a kan mulki. An haife ni a watan Janairun 1970 kuma na san dangin Gnassingbe da ke mulki.”

Shi kuma Ayaovi Sohou dake zaman dan kasuwa cewa ya yi, “Babu ayyukan yi ga matasa, suna cikin halin kaka-nika-yi, kasar nan ba ta da kyau kuma mun gaji da tsarin da ake yi, a wannan karon babu wanda zai yaudare mu da alkawurran da ba a taba cikawa ba. Yanzu idanuwanmu sun bude.”

Gyaran tsarin mulkin da ‘yan majalisar suka amince da shi a ranar 19 ga watan Afrilu, ya sa shugaban kasa yin wani biki.

Yanzu dai majalisar dokoki ce za ta zabi shugaban kasa ba al’umma ba, na tsawon shekaru hudu.

Ikon zai kasance tare da shugaban majalisar ministocin, wani nau'in firayim minista wanda ke zama shugaban jam'iyya mai rinjaye a sabuwar majalisar.

Idan jam'iyya mai mulki ta Union for the Republic -- wacce ke da rinjayen 'yan majalisa -- ta yi nasara a ranar Litinin, Gnassingbe na iya karbar sabon mukami.

Masu suka dai sun ce hakan zai ba shi damar tsallake dokar wa'adin mulkin shugaban kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG