Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burkina Faso Ta Dakatar Da VOA Daga Watsa Labarai A Kasar


Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore
Shugaban mulkin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore

Kakakin VOA Nigel Gibbs ya ce VOA ta rufe tashar FM dinta a Ouagadougou, babban birnin Burkina Faso, sakamakon dakatarwar.

Mahukunta a Burkina Faso sun dakatar da ayyukan Voice of America (VOA) a kasar tsawon watanni uku saboda wasu kalaman da daya daga cikin ma’aikatanta ya yi.

Gwamnatin sojin da ke mulkar kasar ta kuma dakatar da kafofin watsa labarai na cikin gida daga amfani da duk wani rahoto daga kafofin watsa labarai na kasashen duniya.

Majalisar Kula da Sadarwa ta Burkina Faso, ko CSC, ta zargi VOA da karya wa sojojin kasar kwarin gwiwa a Burkina Faso da kuma makwabciyarta Mali a cikin wani shiri da aka watsa a ranar 19 ga Satumba, a cewar rahotannin kafofin watsa labarai.

Wannan hirar daga bisani wani gidan rediyo mai zaman kansa na cikin gida ya sake watsa ta, in ji Reuters.

A cikin wata sanarwa ta imel, kakakin VOA Nigel Gibbs ya ce VOA ta rufe tashar FM dinta a babban birnin Burkina Faso, Ouagadougou, sakamakon dakatarwar.

"Amma, duk da cewa VOA tana mutunta tsarin dokoki na cikin Burkina Faso, ba mu amince da kalaman da Majalisar Kula da Sadarwa ta yi ba domin suna cike da kuskure.” In ji Gibbs.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG