A yau daya ga watan Fabrairu, Hadakar kungiyoyin Mata a Musulunci suka bude taron karfafa wa mata sa hijabi da ake gabatarwa a Najeriya wato “World Hijab Day” a Turance.
Taken taron na wannan shekarar shine “Mata su zamanto daya a duk inda suke” wato “Unity In Diversity” a Turance.
Taron, wanda ya samu sukar lamiri da banbance-banbancen fahimta daga wasu ‘yan uwa mata, ya ga mata da yawa.
Shugabar Kungiyar Mata Masu Da’awa ta Najeriya kuma daya daga cikin wadanda suka shirya taron, Rahma Musa Sani, ta ce, akan shirya taron ne don wayar da kan mata game da muhimmancin saka hijabi, ganin yadda ake musguna wa mata masu sa hijabin a wasu guraren aiki.
Daya daga cikin mai sukar lamirin taron, Malama ce mai koyar da mata a Birnin Tarayya Abuja, Fatima Laminu, wadda ta ce, ya kamata mata su dage wajen neman ilimi, sannan ta ce, taron bashi da asalin a Musulunci.
Shugaban Majalisar Malamai a Abuja, Sheik Ibrahim Muhammad Duguri (Sarkin Malaman Duguri) ya ja hankalin mata tare da bayyana cewa a shari’ance babu wata rana da aka ware ta hijabi domin duk mace Musulma ya kamata a ce tana cikin hijabi a duk lokacin da za ta fita.
Saurari cikakken rahoton wakiliyar Muryar Amurka, Hauwa Umar:
Facebook Forum