Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas Ta Gindaya Sharuddan Saka Hijabi a Makarantu


Wasu mahalarta taron ranar Hijab ta Duniya a Abuja
Wasu mahalarta taron ranar Hijab ta Duniya a Abuja

Sanarwa ta kara da cewa duk da cewa an amince a saka hijabin, dole sai ya zamanto “gajere, tsabtatacce, kuma ya kasance launinsa ya yi daidai da launin kayan makarantar.”

Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta ba da umurnin cewa Musulmai dalibai mata, za su iya ci gaba da saka hijabi a makarantu.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar ta hannun ma’aikatar ilimin jihar ta ce za a iya barin dalibai mata su saka hijabin, har sai lokacin da kotu ta yanke hukunci kan lamarin.

Yanzu haka shari’ar na gaban wata kotun koli.

Sanarwa ta kara da cewa duk da cewa an amince a saka hijabin, dole sai ya zamanto “gajere, tsabtatacce, kuma ya kasance launinsa ya yi daidai da launin kayan makarantar.”

Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa, makarantu su kiyaye yadda suke tafiyar da batun na hijabi da irin matakan da suke dauka wajen yin hukunci.

Batun saka hijabi a makarantun jihar ta Legas, ya haifar da takaddama.

A shekarar 2016, wata kotu ta yanke hukuncin cewa a bari dalibai mata su rika saka hijabi, hukuncin da wasu rahotanni suka ce gwamnatin jihar ta daukaka kara akai.

Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril, daga Legas:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG