Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa barazanar dake tattare da ta’ammali da miygun kwayoyi ta zarce wacce ke tattare da matsalar tsaro da ta ‘yan tawaye da suka addabi wasu sassan arewacin Najeriya.
Shugaban ya ce, lamarin ya zama ruwan dare gama duniya yana mai cewa matsalar ta fadada har zuwa matakai uku wato daga kan kaka, iyaye da ‘yayansu.
Sakataren Gwamnati tarayya Boss Mustapha ne ya yi wannan bayanin yayin da ya wakilci shugaba Buhari a wurin kaddamar da wani shirin yakin da al'amuran da suka sahfi amfani da miyagun kwayoyin da aka mai take da WADA.
Kaddamar na zuwa ne a yayin da aka yi bikin yaki da ayyukan miyagun kwayoyi da Majalisar Dinkin Duniya ta ware na 26 ga watan Yuni.
Wannan bayani na shugaban na zuwa ne a daidai lokacikn da NDLEA ta bayyana cafke akalla masu safarrar miyagun kwayoyi zuwa kasashen ketare 2, 180, cikinsu, har da gaggan masu wannan harkar 5 cikin watanni 5.
Shugaba Buhari ya ummarci NDLEA da Kara kaimi wajen fatattakan muggan irin da suka tare a dazuka kuma suke addabar yankunan kudu maso yammacin Najeriya baya ga noma tabar wiwi.
Ya kuma ba NDLEA umarnin ta kirkiro hanyoyin aiki da al’umma ta yadda za a kai ga rusa masu wadannan munanan ayyuka, sannan a wayar da kan al’umma kan illar amfani da miyagun kwayoyi.