Alkalan kasashe masu iyaka da teku na Afirka ta yamma sun yi taro a Abuja don nazari wajen karfafa dokokin hukunta ‘yan fashin teku da kan kawo barazana ga masu hada-hadar kasuwanci da zuba jari a bangaren.
Taron dai ya tara manyan alkalai na kasashen don bani gishiri in ba ka manda kan dokokin da hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa ta Najeriya. Najeriya ba ta da irin wadannan dokoki a tsarin mulki da za a rika amfani da su don katse hamzarin ‘yan fashin tekun da kan takurawa ‘yan kasuwa.
Babban alkalin kasar Gambia Hassan Boubacar Diallo ya ce dokokin da a ke amfani da su a kasashen tun zamanin mulkin mallaka aka tsara su don haka akwai bukatar sabunta su don su dace da zamanin yau.
Boubacar Diallo ya ce akwai muhimmancin samun dokoki masu kwari don lamarin ‘yan fashin teku ya shafi dukkan kasashen duniya ne.
Shugaban hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa ta Nigeria Hassan Bello ya ce rashin dokoki masu kwari na kawo gagarumar asara ga Nigeria ta hanyar fargabar masu zuba hannun jari da ke dari darin cin karo da barayin tekun.
Bello ya ce bayan taron za a tara dukkan shawarwari na dokokin a mikawa majalisar dokoki don dubawa da yiwuwar maida su kundin doka.
Wani kwarerre a lamuran zuba jari a Nigeria Muhammad Kashim ya ce da zarar an samu kwararan dokoki Nigeria za ta kara bunkasa ta fannin dinbin lamuran raya arziki da ke zuwa daga hada-hadar teku.
Alkalai da dama daga babbar kotun tarayyar Nigeria da tekwarorinsu na Afirka masu magana da harshen Ingilishi sun halarci taron.
A saurari karin bayani a rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Facebook Forum