Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Bai Halarci Jana’izar Attahiru Ba Ne Saboda Ba Ya Son Ya Haifar Da Cunkoson Ababen Hawa – Garba Shehu


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Twitter/@BashirAhmaad)
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Twitter/@BashirAhmaad)

 “Dalilin kenan ma da ya sa yake Sallar Juma’a a fadarsa, maimakon ya je Masallaci.” In ji Garba Shehu.

Malam Garba Shehu, Kakaki ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fito ya kare shugaban kan dalilin da ya sa bai halarci jana’izar babban hafsan sojan kasar Laftarnar Janar Ibrahim Attahiru da aka yi hade da wasu sojojin kasar 10 ba.

A ranar Asabar aka gudanar da jana’izar, bayan hatsarin jirgin da ya yi sanadin mutuwar manyan sojojin a jihar Kaduna da ke arewa maso yammaci.

An binne mamatan ne a makabartar dakarun kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Amma rashin halartar Buhari ko mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo wajen jana’’izar, ya haifar da ka-ce-na-ce a tsakanin ‘yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

‘Yan Najeriya da dama sun raja’a ga nuna rashin dacewar kin halartar shugabannin wajen jana’izar.

Ko da yake, wasu sun nuna cewa ba laifi ba ne don shugaban bai halarci jana’izar ba, domin a cewarsu, ya tura wakilai.

Sai dai Malam Garba Shehu ya fadawa gidan talabjin na Arise cewa, a “fahimtarsa,” Buhari ya kauracewa wajen jana’izar ne, gudun kada a rufe hanyoyi da za su kai ga haifar da cunkoson ababen hawa a Abuja.

“Buhari ba ya son a rika rufe hanyoyi, ko jami’an tsaro su rika cin zarafin wadanda ba su ji ba ba su gani ba, don kawai ana so a sama wa shugaban kasa hanya.” Shehu ya ce.

Kakakin shugaban ya kara da cewa, an yi jana’izar da safe ne, “saboda haka ba ya so ya dauke hankalin mutane daga abin da ke faruwa.”

“Dalilin kenan ma da ya sa yake Sallar Juma’a a fadarsa, maimakon ya je Masallaci.” In ji Shehu.

A ranar Lahadin da ta gabata,
Buhari ya gana da mai dakin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, Hajiya Fati Ibahim Attahiru da sauran iyalan sojojin da suka rasu a hatsarin jirgin da ya faru a Kaduna.

Sannan gabanin hakan, uwargidansa Aisha Buhari, ta kai ziyarar ta’aziyya gidan marigayi Attahiru, a wani abu da wasu ke ganin, yunkuri ne na yayyafa ruwan sanyi kan sukar da fadar shugaban kasar ke fuskanta a lokacin.

XS
SM
MD
LG