Kungiyar Transparency International dake fafutuka yaki da cin hanci da rashawa na ganin idan al’umar Najeriya, sun sami amincewa da shuwagabanin su da a halin yanzu ke kokarin cin hanci da rashawa toh ya zama wajibi a garesu su taka rawa wajen marawa shuwagabanin baya domin kasa ta gyaru.
Jami’in kungiyar mai kula da shiyar Afirka, ta yamma, yace akwai dalilai da suka kungiyar yin wannan taron, domin mun yi Imani cewa ta hanyar tattaunawa ne za’a jawo hankalin al’uma domin duba hanyoyin da suka fi dacewa domin shawo kan cin hanci da rashawa, abinda yasa kungiyar ta hada kan huikumomi domin karfafa masu guiwa wanda yin hak zai sa mu samu karfafawa al’umar kasa guiwa domin su taya shuwagabanin su yaki da cin hanci da rashawa.
Daya cikin wadanda suka halarci taron kuma tsohon shugaban kungiyar kari hakkin bil Adama a Najeriya, Buhari Bello, yace dole ne ‘yan kasa dake shugabantar kungiyoyin cin hanci da rashawa suyi kokari wajen taimakawa shuwagabanin su idan ana so kasa ta ci gaba.
Ya kara da cewa yakamata a fara darasi akan cin hanci da rashawa da firamari har zuwa jami’a, domin cimma nasarar yaki da wanna annobar.
Kungiyar Transparency International, tace mutane hamsin da biyar a Najeriya sun sace kudi har Naira, Trillion daya da Billion dubu dari hudu wanda yasa Najeriya ta kasance kasa ta dari da talatin da shida daga cikin kasashe dari da sittin da takwas wadanda aka kiyasta suna da matsalar dabi’un cin hanci da rashawa, koda yake a yanzu ta cimma kasha ashirin da shida a nasarar yaki da wannan mummunar dabiya.