Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'umar Jihar Filato Ta Bukaci Hukumomi Da Malaman Addinai Da Kungiyoyi Su Hada Kai


A taron kallon fayafayan bidiyo da gidan radiyon Muryar Amurka ya fitar da aka yiwa lakabi da Tattaki daga bakar akida, jama'ar jihar Filato sun yi kira ga daukacin al'umar jihar domin hada kai wajan shawo kan matsalar data ki ci taki cinyewa a wasu sassan jihar.

Al’ummomi a jihar Filato, sun bukaci hukumomi da malaman addinai da kungiyoyi masu zaman kansu su hada kai wajen magance matsalar makiyaya da manoma da ta addabi shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya.

A taron majigi da gidan radiyon Muryar Amurka ya gudanar a Jihar Filato masu ruwa da tsaki sun yabawa Muryar Amurka bisa kokarinta na hada wannan faifan bidiyo inda suka ce zai taimaka kwarai wajen yaki da fitintunu dake aukuwa a Najeriya.

Wani mutum mai suna Sani sulaiman, ya bada bayani kan cewa faifan bidiyon ya bada tsokaci da lura mai kyau wadda zata taimaka wajen samar da waraka ga matsalolin tashin hankali, haka kuma Pharmasist Marcus Audu, shugaban matasan kirista a jihar ta Filato yace idan za’a iya samu a nunawa matasa wannan majigi a Choch-chochi da Masallatai, a kuma yi gargadin cewa rashin zaman lafiya baya taba kawo alheri toh abin zai yi tasiri sosai.

Malam Sani Mudi, mai magana da yawun kungiyar Musulmi yace lalacewar ilimi a Najeriya na daya daga cikin abubuwan da suka samar da Boko Haram, har ta kafu dan haka gwamnati ta bada karfi akan wannan musamman ilimin addini.

Shugaban kungiyar addinin Kirista a jihar, Reverend Soje Beweren, yace jama’a suyi hakuri su zauna lafiya domin Allah yayi su don su zauna tare kana shugaban gidan rediyo da talabijin mallakar jihar filato Jefta Jackdin, yace ya kamata suyi koyi da majigin, kwamishinan yada labarai Muhammad, ya bayyana cewa ya kamata hukumomi su binciki inda mahara ke samunn kayan aikinsu wato makamai, abinci, motoci, magunguna da sauran su domin magance matsalar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG