Madugun kungiyar Boko Haram ya dauki alhakin kai wani harin bom kwanan nan a garin Lagos, idan ta tabbata gaskiya, wannan ne zai zama karon farko da kungiyar ta 'yan ta'adda ta kai hari cikin birnin kuma cibiyar hada-hadar kasuwancin Najeriya.
A cikin wani sabon bidiyon da ya bayyana a yau litinin, Abubakar Shekau na cewa shi ne ya tura maharin da ya je Lagos ya farfasa boma-bomai biyu a wata matattarar mai a ranar 25 ga watan yuni, ya hallaka mutane biyu a kalla.
Gwamnati ta ce fashe-fashen sun wakana ne a lokacin sanadiyar fashewar wani bututun gas. Game da wannan bayani na gwamnati, Shekau ya bushe da dariya, ya ce idan za ku iya boyewa jama'a gaskiya, ba za ku iya boyewa Allah ba.
Haka kuma madugun na Boko haram ya dauki alhakin fashewar bom din kwanakinbaya a Abuja wanda ya hallaka mutum 24.
Bidiyon wanda babu kwanan wata a jiki, ya na dai nuna Shekau ya na magana da Hausa, 'yan bindiga 12 sanye da hulunan badda kama su na kewaye da shi.
Nan take dai babu wani martani ko bayani daga 'yan sandan Najeriya ko gwamnatin kasar.
Idan Boko Haram ta kai hari cikin Lagos abun zai yi matukar tayar da hankali, saboda birnin na daga cikin biranen Najeriya mafiya girma, kuma ya na da mutane kimanin miliyan 20.
Yawanci dai Boko Haram na kai hare-haren ta a wajejen sansanin ta na asali a yankin arewa maso gabashin kasar. Kungiyar aka dorawa laifin hallaka dubban jama'a a cikin shekaru biyar da suka gabata.