A yayin wata ganawa ta musamman da wasu kafofin labarai a Kano jakadan Amurka a Najeriya ya tabo batutuwa da dama kama daga batun Boko Haram, zabuka da kasar zata gudanar badi da sauran alamura da suka shafi tattalin arziki da harkokin ilimi a Najeriya.
Dangane da tallafin da Amurka tace zata baiwa Najeriya akan 'yan matan Chibok da 'yan Boko Haram suka sace sai jakadan yace ba zai zurfafa magana ko bada cikakken bayani ba akan halin da ake ciki da wannan batun. Yace amma sun cimma wani nikafi ta fuskar musayar bayanai a kokarin dafawa gwamnatin Najeriya domin ta ceto yaran.
Jakadan ya kara da cewa baya ga wannan, suna aiki tare da hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya wajen tallafawa dubban mutanen da rikicin Boko Haram ya tagayyara a yankin arewa maso gabashin kasar.
Jakadan ya cigaba da cewa haka kuma suna wasu abubuwa wadanda a fahimtarsu zasu murkushe ayyukan tarzoma domin kuwa abun ya wuce batun yin anfani da soja kawai.
Akan zabukan da za'a yi shekara mai zuwa jakadan cewa yayi suna aiki tare da kungiyoyin fafitikar wanzar da dimokradiya inda yanzu haka suna bada horo ga kungiyoyi dake aikin sanya ido akan harkar gudanar da zabe. Yace mafi mahimmanci shi ne yadda za'a yi zabe cikin lumana ba tare da tarzoma ba. Sabili da haka jakadan yace yana kiran 'yan siyasa da su fito fili su nuna suna kyamar tarzoma ko tada hankalin jama'a a lokacin zabe ko kuma bayan an gudanar da zaben.
Jakadan yace a wasu lokuta wasu manyan 'yan siyasa sun taba fada masa cewa ba zasu iya bada tabbacin ba zasu tada hankali ba domin watakila bukatar su yi hakan ka iya tasowa nan gaba. Jakadan yace kalamunsu abun bakin ciki ne.
Kafin ganawa da manema labarai sai da Jakadan ya gana da mai marta Sarkin Kano Malam Sanusi Lamido Sanusi II da gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.