Sauran sassan Najeriya sun yi watsi da bukatar Niger Delta amma sun amince da karin kashi 5 cikin dari akan kason da aka ware masu yanzu.
Tun lokacin gwamnatin Obasanjo kawo yanzu kaso goma sha uku suke samu. Idan an kara kaso 5 cikin dari zasu tashi da kaso 18 ke nan.
Wannan takadda da taron ya shiga ka iya kaiga kada kuri'a. Idan aka kada kuri'a da wuya 'yan arewa su yi nasara. Fati Ibrahim Yunus wakiliya ce daga kungiyar tuntuba ta arewa tace karin kashi 5 cikin dari da ya basu kashi 18 sai suka dinga ihu suna tada hankali. Tun da lamarin haka yake tace a je a kada kuri'a idan an kayar da arewa su san an kayar da su maimakon ace arewa ta yadda da bukatunsu.
Inji Fati Ibrahim zasu cigaba da taron yau amma babu wanda ya san yadda zata kaya. Watakila a yi zabe. Tace ba zasu yadda da kuri'ar murya ba kawai domin ana iya cutar wani bangare. Idan za'a yi zabe kuri'a za'a kada a kuma kirga.
Wakili daga arewa maso gabas Isa Tafida Mafindi yace arzikin arewa ya fi martabar man fetur. Arewa nada kasar noma kuma tana iya ciyar da kasar da ma Afirka gaba daya. Lokaci yayi da arewa zata tashi ta fuskanci noma gadan gadan. Arewa ta cuci kanta. Tana wauta. Tana duban wani maimakon ta habbaka nata tattalin arzikin. Yakamata arewa ta zauna ta sake duban kanta.
Idan an dawo taron yau za'a karawa jihohin arewa kaso uku cikin dari domin gyara komatsar da kungiyar Boko Haram ta haddasa.
Ga karin bayani.