Biyo bayan yadda masu zaben raba gardama a kasar suka zabi fincike kansu daga cikin kungiyar tarayyar Turai, lamarin da aka bayyana a matsayin abinda ya ruda kasar da rabonta da ganin haka tun bayan yakin duniya na biyu.
A kokarin kwantar da hankalin Birtaniyawan game da rudanin, Ministan harkokin kudin kasar yace, tattalin arzikin Birtaniyya fa yana da karfi tun asali, sannan kofofin kasar a bude suke game da harkokin kasuwanci kamar yadda aka saba.
A dukudukun Litinin din nan dai kasuwanin hada-hadar kudi a Turai suna ta tangadi, sai dai ba kamar yadda aka gani a ranar Juma’a ba, lokacin da kasuwar hannayen jarin birnin London ta yi kasa da kaso 8, kafin daga baya ta dan farfado da kaso 3.