Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dar Al-Hijrah Na Buda Baki Har Da ‘Yan Majalisar Dokokin Amurka


Wasu Masu Buda Baki a Masallacin Dar Al-Hijrah, Karamar Hukumar Falls Church Da Ke Jihar Virginia Ta Amurka
Wasu Masu Buda Baki a Masallacin Dar Al-Hijrah, Karamar Hukumar Falls Church Da Ke Jihar Virginia Ta Amurka

Masallatai da yawa a jihohin Amurka na shirya liyafar buda baki ko kuma mu ce shan ruwa bayan an kai azumin kowace rana. Dar Al-Hijrah ma na daya daga cikin cibiyoyin musulmi da ke karamar hukumar Falls Church a jihar Virginia ta Amurka.

Wannan waje cibiya ce mai hade da masallaci da kuma makarantar Islamiyyar yara da manya domin karatun addinin musulunci da kuma aiwatar da sallolin farilla guda biyar a rana kamar yadda yake a musulunci.

A jiya Alhamis sha 18 ga watan Ramadan, wanda yayi daidai da 23 ga watan Yunin shekarar nan ne muka ziyarci wannan masallaci, don tattaunawa da daya daga cikin mahalarta ko shirya irin wannan buda bakin da ake yi a masallatai don taimakon juna da masu karamin karfi.

Mun tattauna tare da wani Muhammad dan asalin kasar Saudi Arabiya da ya zo nan Amurka shekaru 4 da suka wuce. Ya kuma amsa mana tambayar yadda yake ji game da irin wadannan cibiyoyin da ake buda baki da azumi. Inda yace, hakika abu ne mai kyau sosai, domin yana cusa hadin kai tsakanin musulmi.

Daga nan kuma sai muka tattauna da daya daga cikin jiga-jigan wannan cibiya mai suna Malam Abdulkadir Usman Ahmad. Ya kuma bayyana mana yadda wannan abu yake da muhimmanci, na taruwa ayi buda baki. Har ya kara da cewa, baya ga buda bakin da musulmi ke taruwa suna yi a kullum cikin azumi.

Yace duk ranar Laraba a watan azumin, su kan gayyaci makwabtansu wadanda ba musulmai ba a unguwar ta Falls Church, tare da wasu daga cikin ‘yan majalisun dokokin Amurka, don yin buda baki tare da su. Ya rufe da cewa, hakan yana da matukar muhimmanci ga tsaron kasa da kawo hadin kai tsakanin mai wani addini da wani da ba irin nasa addinin yake yi ba.

Duk wannan hidimar buda bakin da ke ciyar da mutane fiye da guda 1000 a rana, ana samun kudin hidimar buda bakin ne daga kudin sadakar da al’umma ke bayarwa.

Ga kadan daga tattaunawarmu da daya daga mahalarta shan ruwan Malam Muhammad dan kasar Saudiyya. Da kuma shi jigo a masallacin, wato Malam Abdulkadir Usman Ahmad, wanda muka gana bayan an sha ruwa an kuma yi sallah.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG