Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukuncin Birtaniya Na Ficewa Daga Kungiyar Tarayyar Turai


Wasu Yan Birtaniya na tafiya bayan sun kada kuri'ar su
Wasu Yan Birtaniya na tafiya bayan sun kada kuri'ar su

Birtaniya ta yanke hukunci na tarihi inda ta fice daga kungiyar tarayyar Turai ta hanyar kada kuri’ar raba gardama da aka gudanar bisa la’akari da batun shige da fice da diyaucin kasa, matakin da ya sa Fara Ministan Birtaniya David Cameron yin murabus.

Cameron ya shaidawa manema labarai a bakin fadar gwamnati dake lamba 10 titin Dwoning yau jumma’a cewa,” al’ummar Birtaniya ta tsaida shawara karara ta kama wata hanya ta dabam, saboda haka, ina jin kasar tana bukatar sabon shugaba da zai kai ta gaci.

Cameron yace zai ajiye aiki a watan Oktoba.

Masu sharhi kan lamura sun ce, kada kuri’ar da jama’a suka yi na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai manuniyace cewa, Camaron bashi da goyon baya. Mutumin da ya jagoranci gamganin ficewa daga kungiyar Boris Johnson, wanda shima dan jam’iyar Cameron ta ‘yan mazan jiya ne, ake kyautata zaton zai maye gurbin Cameron a matsayin Fara Minista.

Kimanin kashi 72 cikin 100 na al’ummar kasar da suka cancanci kada kuri’a ne suka fito, adadi mafi girma a tarihin zaben kasar cikin shekaru ashirin, duk da ruwan saman da aka rika tafkawa kamar da bakin kwarya ranar kada kuri’ar raba gardamar,abinda ya nuna irin yadda batun ya tada tsimin jama’a a kasar da aka sami rubin adadin ‘yan ci rani dake kwarara kasar cikin shekaru goma sha shida da suka shige.

Ana gani an kada kuri’ar ne a dalilin nuna gajiya da ‘yan siyasa da kuma tunanin cewa, kungiyar tarayyar Turai ta kwace iko daga talakawan Birtaniya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG