Ministan makamashin kasar Saudiyya ya ce hare haren jiragen sama marasa matuki akan kamfanonin sarrafa man Aramco guda biyu da aka kai a Saudiyya sun sa za a rage ayyukan hakar mai da rabi yanzu.
Wani hoton bidiyo na harin da aka kai tun da sanyin safiyar jiya Asabar a Abqaiq, dake gabashin Saudiyya, ya nuna yadda wuta ta yi ta ci a wurin. Zuwa rana kuma, bidiyon ya nuna hayaki na tashi sama. Jami’an kasar Saudiyya dai sun ce babu ma’aikacin da ya rasa ransa ko ya jikkata a hare-haren.
Wani mai magana da yawun mayakan Houthi na Yemen, kanal Yahya Saree, ya dauki alhakin kai hare-haren na jiragen sama na jiya Asabar akan kamfanonin man Saudiyya, ya kuma yi alkawarin zasu kara kai hare-haren idan har dakarun kasashen da Saudiyyar ke jagoranta suka ci gaba da kai farmaki akan mayakan dake Yemen. Ko da yake, babu tabbacin ko daga Yemen jiragen saman suka taso.
Saree ya kuma yi ikirarin cewa harin na jiya shine mafi girma da suka kai ya zuwa yanzu kuma ya bukaci nazari da bayanan sirri sosai, ciki harda wasu bayanai da suka samu daga wasu mutane a cin Saudiyya.
Facebook Forum