Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zizi Kodwa Ya Zargi Gwamnatin Amurka Da Taimakawa Wajen Kame Mandela


Zizi Kodwa, Kakakin jam’iyya mai mulki a Afirka ta Kudu.
Zizi Kodwa, Kakakin jam’iyya mai mulki a Afirka ta Kudu.

Kakakin jam’iyya mai mulki a Afirka ta Kudu ya zargi gwamnatin Amurka da laifin kalubalantar zababbiyar gwamnatin kasarsu. Duk da yake dai wakilai daga bangarorin kasashen biyu sun yi watsi da zargin tare da cewa alakarsu da karfinta.

Furucin Kakakin jam’iyyar ta ANC Zizi Kodwa, ya biyo bayan wani labari ne da jaridar karshen mako ta British Sunday Times ta buga, na cewa, Ma’akatar Leken Asirin ta CIA dake Amurka ta taimakawa gwamnatin wariyar wajen kama Nelson Mandela a 1962.

Rahoton da ya gutsuro maganar wani marigayin mai ritaya a ma’aikatar ta CIA da yace, Amurka ta kalli Marigayi Mandela a matsayin wani mai goyon bayan ‘yan ra’ayin gurguzu.

Mandela sai da ya shafe shekaru 27 a gidan yari, kama daga gwamnatin wariyar launin fata zuwa kan ta wadanda yake adawa da su a siyasance. An kuma zabe shi a matsayin shugaban kasa bakin fata na farko a shekarar 1994.

Kodwa ya fadawa kafofin yada labaran cikin kasar, cewa har yanzu ma’aikatan leken asiri CIA suna like da su suna kuma taimakawa masu son canjin gwamnati a kasar. Muryar Amurka ta so jin ta bakin Mista Zizi, amma ya ki daukar wayoyin da aka yi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG