Jakadan Amurka a Najeriya James F. Entwistle, ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda yaga matasan yan Najeriya guda 100 na ta zumudi da dokin tafiya Amurka a shirin nan na horas da matasa da Amurka ke daukar nauyi duk shekara wato YALI.
Entwistle ya bayyana gamsuwarsa kan yadda matasan baya suka ci moriyar wannan shiri, kuma suke bayar da gudunmawarsu a sassa daban daban na Najeriya, a watan Disambar da ta wuce ne matasan da suka amfana da wannan shiri suka kai gudunmawar kayan agaji da ya hada da Tufafi da Barguna a sansanonin yan gudun hijira dake Maiduguri.
Jakadan ya kuma yi tsokaci kan dalilan da yasa aka kirkiro wannan shiri, inda yace wannan shirin horaswa na Mandela Washington Fellows ga matasan Afirka, wani kokarin shugaba Barack Obama ne na kyautata makokamar Afirka, bisa gamsuwa da shirin ne yasa aka kara adadin mahalarta a bana daga 500 zuwa 1000 a wannan shekara.
Fadar White House ta kirkiri wannan shiri ne bisa yin na’am da irin rawar da matasan Afirka ke takawa na karfafa turakun tsarin dimokaradiya da habaka tattalin arziki da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.
Balarabe B Isma’il, dan asalin jihar Kano ne da ya samu shiga cikin wannan shiri, inda yace, “zanje Jami’ar jihar Ohio dake Columbus, kuma ina godiya ga gwamnatin Amurka da kuma dukkannin wadanda sukayi addu’a da bayar da gudummawa wajen samun wannan nasara.”
Domin karin bayani.