Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bidiyon Maryam Booth Da Adam Garba Ya Ja Hankalin Masoya Fina-finan Kannywood


Adam Garba, hagu, Maryam Booth, dama (Hoto: Instagram/Maryam Booth)
Adam Garba, hagu, Maryam Booth, dama (Hoto: Instagram/Maryam Booth)

Bidiyon na dauke da jaruman biyu cikin yanayi na farin ciki, ya kuma yi kama da hotunan da amarya da ango kan dauka gabanin aure wanda ake kira “pre-wedding pics.

A karshen makon da ya gabata ne jaruma Maryam Booth ta wallafa wani bidiyo wanda ya nuna yadda suka caba ado da ita da jarumi Adamu Garba na shirin Labarina, wanda ya fito a matsayin “Raba Gardama.”

Bidiyon na dauke da jaruman biyu cikin yanayi na farin ciki, ya kuma yi kama da hotunan da amarya da ango kan dauka gabanin aure wanda ake kira “pre-wedding pics.”

Kazalika an ga jarumar ta rubuta a kasan bidiyon cewa “Dear Husband” wato “Ya Mijina” hade alamar zuciya da ke nuna soyayya.

Ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin, mutum sama da dubu 25 ne suka nuna kauna ko liking ga bidiyo wanda yake dauke da wakar Namenj da ake kira “Gani.”

Wasu daga cikin wadanda suka yi sharhi kan bidiyon sun yi ta yi wa jaruman biyu murnar Allah ya ba da zaman lafiya.

Wasu kuwa sun yi nuni da cewa ba aure za su yi ba fim ne.

A wasu lokuta jarumai kan dauki irin wannan bidiyo ko hoto su yada a shafukansu na sada musamman a lokutan da ake daukan wani fim dan janyo ce-ce-ku-ce.

Dandalin Mu Tattauna

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG