Tarar da hukumar kare bayanai ta Ireland ita ce mafi girma tun lokacin da Tarayyar Turai, ta aiwatar da tsauraran tsarin tsare bayanan sirri shekaru biyar da suka gabata.
Adadin tarar ta fi girma fiye da hukuncin dala biliyan 800 na kamfanin Amazon, a cikin shekarar 2021 don keta kariyar bayanai.
Cibiyar sa ido ta Irish ita ce jagorar sirrin Meta a cikin kungiyar kasashe 27 saboda babbar hedkwatar ta Turai ta fasahar Silicon Valley ta kasance a Dublin.
Kamfanin Meta ya ce zai daukaka kara kan hukuncin, kuma ya bukaci kotuna da su gaggauta dakatar da hukuncin.