Masu gabatar da kara a kotun manyan laifuka ta kasa da kasa, sun ce za su daukaka kara saboda wanke tsohon Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo da aka yi daga laifin cin zarafin bil’adama, game da munanan tashe-tashen hankulan da su ka biyo bayan faduwarsa zaben shugaban kasa a 2010.
Kwamitin alkalai uku ya bayar da umurnin a saki Gbagbo da hadiminsa kuma tsohon Ministan Matasa na kasar Charles Ble Goude ba tare da bata lokaci ba, to amma an jinkirta aiwatar da umurnin zuwa yau Laraba saboda a bai wa masu gabatar da kara cikakken lokacin daukaka kara.
A martaninsu ga kotun, masu gabatar da karar sun bukaci da alkalan su gindaya tsauraran sharudda game da sakin na Gbagbo da Goude, su na masu nuni da yiwuwar su gudu idan su ka ga an yi nasara a daukaka karar.
Facebook Forum