Cudanyar yara a cikin aji yasa tun farko ministan ilimi Ibrahim Shekarau ya daga ranar komawar yara makaranta zuwa watan gobe. Amma kuma daga bisani ya rage zuwa 22 ga wannan watan sabili da nasarar da kasar ta samu na fatattakar cutar ebola daga kasar.
Sani Tahir yana cikin iyayen yara da suka goyi bayan tsawaita hutun. Yace yaya suke tsammani zasu kare 'ya'yansu idan an barsu a makaranta. Akwai rigakafin cutar shan inna da wasu amma me yasa ba'a samu ta ebola ba. Tun da sun ce suna bincike sai iyaye su tsaya su gani idan an kai wani lokaci babu wani abu to ana iya cewa yara su koma makaranta. Shi yana ganin cutar tana kara yaduwa. An fara tun daga shida yau kasar na wurin goma sha.
Dan majalisar tarayya Abdulrazak Zaki yace tabbas majalisa zata duba batun hutun yaran da zara ta dawo zama makon gobe. Yace alamura na nan birjik a gaban majalisar. Da sun dawo zasu fada kansu. Akwai maganar komawar 'yan makaranta bakin karatu sabili da bala'in ebola. Tsakanin ashirin ga wannan watan da sha uku na watan gobe duk banbancin 'yan makonni ne. Allah dai ya sa an kawo karshen cutar. Ba zata wuce inda ta tsaya a Legas da Fatakwal ba.
Likitan asibitin gwamnatin tarayya dake Birnin Kudu jihar Jigawa Dr. Shamsudeen Sani yace maganar gaskiya ita ce kasar ba zata iya buga kirji tace ta shawo kan cutar ba iyaka dai bata kai tsananin yadda ake tsammani ba. Ma'aikatar ilimi da ta kiwon lafiya ya kamata su hada hannu su tabbatar suna yin abu daya.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.