Malam Abdullahi Jibril shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu kuma sarkin makafin jihar Bauchi shi ya jagoranci addu'ar.
Yayi bayani akan makasudin taron addu'ar. Na farko sun yi taron addu'ar ne saboda neman zaman lafiya domin Najeriya ta zauna lafiya. Irin asarar rayukan da ake yi yasa suka koma ga Allah domin Ya sa a zauna lafiya.
Tashin hankalin ya wuce duk yadda ake tsammani. Yace tashin hankalin bai bar musulmi ba ko kiristoci duk ana kashesu. Ba'a bar 'yan kasuwa ba. Ba'a bar sarakuna ba.Ba'a bar 'yan siyasa ba. Ba'a bar sojoji ba.
Wasu mahalarta taron sun kara bayani. Alhassan Tata Muhammed sarkin guragun Ningi kuma sakataren majalisar sarakunan nakasassun jihar Bauchi yace sun yi taron domin gabatar da addu'a wa kasa da jihar Bauchi da fatan zaman lafiya domin Allah ya kawar da fitintinun dake addabar arewa maso gabas.
Garba Ibrahim galadiman makafin Bauchi yace taron addu'ar yayi armashi fiye da yadda ake tsammani. Sun roki Allah ya yaye ma kasar duk fitinun dake damun kasar.
Ga rahoton Abdullwahab Muhammed.