Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 19 ne Kawai Suka Kamu da Cutar Ebola a Najeriya


Ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki a tashoshin fice da shigin Najeriya.
Ma'aikatan kiwon lafiya dake aiki a tashoshin fice da shigin Najeriya.

A firar da wakiliyar Muryar Amurka tayi akan cutar ebola da karamin ministan kiwon lafiyar kasar Najeriya, ya shaida mata cewa kawo yanzu mutane 19 ne kawai suka kamu da cutar a duk fadin kasar

Mutanen 19 da suka harbu da cutar, 15 daga birnin Legas suka kamu kana hudu suka kamu a Fatakwal dake jihar Rivers.

Cikin adadin wadanda suka harbu da cutar mutane 9 sun samu sauki har ma an sallamesu daga asibiti. Mutane 7 sun rasu yayin da ake kula da guda uku.

Akan kirar da Amurka tayi na cewa Najeriya ta taimakawa kasashen yammacin Afirka dake mugun fama da cutar ministan yace sun taimaka da kudi dalar Amurka miliyan uku da rabi zuwa kasar Liberia da horaswa da ma'aikata domin karfafawa wajen bada magani. Yace har yanzu a shirye suke su kara bada taimako bisa ga nasarorin da suka samu na kawar da cutar daga Najeriya.

Dangane da shawarar da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta bayar cewa a yi anfani da jinin wadanda suka warke wajen kula da wadanda suka kamu da cutar sai ministan yace suna nan suna dubawa. Ya kara da cewa jinin wanda ya warke za'a tace a duba irin sojojin da yake jikinsa kana a ba wadanda suke dauke da cutar. Masana a kasar suna aiki akan wannan shirin.

Suna bincike domin a kaucewa kowace illa nan gaba. Akan kudi kalilan da suka baiwa Liberia ministan yace sun yi adalci domin ba su kadai cutar ta shafa ba. Cuta ce da ta shafi duniya gaba daya don haka wasu kasashen su tashi su taimaka.

Ministan yace a shirye suke su je kasashen su yi taimako bisa ga abun da suka sanin yanzu. Suna kuma iya horas da ma'aikatan kasashen da suke makwaftaka dasu domin su yi aiki yadda ya kamata.

Ga cikakken firar da Medina Dauda tayi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG