Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Arzikin Jonathan Siyasa Ce – inji Magoya Baya


Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, yayi amfani da katin shi a naurar Banki na dauki da kanka, 28. Ga Agusta 2014.
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, yayi amfani da katin shi a naurar Banki na dauki da kanka, 28. Ga Agusta 2014.

Wata mujallar kasa da kasa ta bada labarin cewa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na daga cikin attajiran shuwagabannin Afirka, inda shine na 6 a yawan arziki har na dala miliyan 100.

Akan wannan batun ne Aliyu Mustaphan Sokoto na Sashen Hausa a Muryar Amurka ya nemi mai baiwa Jonathan shawara akan harkokin siyasa, Farfesa Rufa’I Alkali.

Rufa’I Alkali yace “yanzu hukumar zabe ta fito da jaddawalin shirye-shiryen zabe da za’a yi a shekara ta 2015, kuma jam’iyyar mu ta PDP ta fito da nata jaddawali na shirye-shiryen zabubbuka da za’a yi anan gaba. Saboda haka za’a ce siyasa ne da za’a yi nan gaba, ya dauki harama”.

“Tunda yanzu siyasa ya dauki harama, to babu abunda baza ka gani ba, kuma babu abunda baza ka jiba. ‘Yan hamayya, zasu ringa bullowa da maganganu daban-daban, da kuma wadanda zasu yiwa shugaban kasa batanci. Naji wannan batu, kuma ‘yan hamayya ne suka bullo da wannan magana, saboda suna gani idan ba haka sukayi ba, baza su iya karya wannan tafiya ba”, inji Mr. Alkali.

Aliyu Mustapha ya tunatar da Farfesa Alkali cewa ba shugaba Jonathan ne kawai aka fito da yawan arzikinshi ba, shugaban Angola ma shine yafi kowani shugaban Afirka arziki. Shima wannan ‘yan siyasan Najeriya suka fitar da wannan labara? Shine Farfesan yace “baka tambaye ni akan shugaban Angola ba, akan shugaban Najeriya ka tambaya. Bazan iya sanin yadda rayuwar shugaban Angola take ba”.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG