Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Barazanar Sauyin Yanayi Kan Noma A Kasashen Afirka


Wasu mata a Uganda su na ban ruwa a wata gona dake Lira.
Wasu mata a Uganda su na ban ruwa a wata gona dake Lira.

Sauyin yanayi yana barazana ga wadansu daga cikin muhimman shuke shuken kasashen nahiyar Afrika da suka hada da masara, da wake da ayaba, abinda masu ilimin kimiyya suka yi gargadi da cewa, akwai bukatar sauyi a tsarin noma da kuma yin wadansu sauye sauye cikin gaggawa.

Matsalar ita ce, sauyin yanayi yana da illar ainun kan shuke shuke a nahiyar, da yasa a wadansu yankuna yanzu haka ba za a iya noma wadansu irin abincin da aka saba nomawa ba.

Jami’ar Leads ce ta gudanar da abinciken da ta buga jiya a mujallar sauyin yanayi da ake kira Nature Climate Change.

Bisa ga rahoton, ba za a iya noma masara da ayaba ba, a kimanin kashi talatin cikin dari na gonakin Afrika a karshen wannan karnin. Banda haka kuma, ba za a iya noma wake ba a kimanin kashi sittin cikin dari na gonakin kasashen nafiyar Afrika.

Shugaban tawagar binciken Dr Julian Ramirez-Villagas daga jami’ar Leeds yace, binciken yana da muhimmanci domin zai taimaka wajen ayyana lokutan da kuma daukar matakan shawo kan barazanar.

Yace abin yi zai hada da canza irin abinda ake nomawa a wuri daya ko kuma a inganta ayyukan noman rani a yankin, a wadansu lokuta kuma, idan matsalar tayi Kamari, abin yi shine a kyale gonaki ba tare da nomasu ba har zuwa wani lokaci.

XS
SM
MD
LG