Na fuskanci matsaloli kamar yadda kowanne dalibi kan fuskanta, mussamam ma daga wajen 'yan-uwa mata, inda wasu daga cikin malaman jami’a kan bukaci daliba ta amince musu domin su bata maki, inda na tabbatar da hakan bai faru a kaina ba, kasancewar na jajirce wajen yin karatu tukuru, ta bakin Malama Hafsa Ibrahim.
Bayan kammala karatu ta samu aiki a lokacin da ta gama yi wa kasa hidima a garin Kano, inda tayi aikin jarida na shekaru 6 daga bisani ta samu aiki da jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, bayan wani dan lokaci ne kuma ta sake samun aiki karkashin Banki duniya wato World Bank a garin Minna.
Ta fuskanci gwagwarmaya a lokacin da take aiki a jami’ar Ahamdu Bello dake Zaria, kasancewar ita kadai ce mace a sashen da take, wato Directorate of University Advancement, inda wani lokaci ko magana tayi sai a dinga katseta ana kashe mata gwiwa.
Malama Hafsa, ta ce duk da kashe mata gwiwa da akeyi, hakan bai sa tayi kasa a gwiwa ba, domin ta jajirce wajen tabbatar da ta kawar da kashe mata gwiwa da suka yi.
A halin yanzu dai tana aikin raya unguwanni da ci gaban jama'a a garin Minna, bayan ta dauki wani hutu na dan lokaci domin ta bautata wa kasar ta
Daga karshe ta ja hankalin 'yan uwa mata da su kasance masu naci da son ci gaban kanasu, su kuma kauracewa masu kashe musu gwiwa wajen ayyukan ci gaba.
Facebook Forum