Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farar Mace Ko Mayya Ce - Ra'ayin Wasu Samari


Yayin da muke zantawa da matasa maza da mata a shirinmu na samartaka musamman kan al'amuran da suka shafi soyayya, zamantakewa da abota tsakanin jinsi, mun sami tattaunawa da wani matashi da ya bukaci mu sakaya sunansa wanda ya bamu takaitaccen bayani akan yadda ya sami kyakkyawar fahimta akan wannan maudu'i, lamrin da ya kwatanta da abin tsoro iya matuka.

Samari da dama sun amince, cewa idan budurwa na da kyau kamar yadda kashi arba'in cikin dari na wadanda muka sami zantawa da su suka bayyana, farar mace koda diyar talaka ce, ta fi nuna kaunar abin duniya fiye da baka. koda shike ba a taru an zama daya ba, da dama sun bada tasu hujjar akan akasin wannan hasashe.

Da alamu 'yan mata masu hasken fata sun fi daukar hankalin samari, musamman matasa a wannan zamani da wasu daga cikin wadanda muka sami zantawa da su suka bayyana cewa sun garace su auri farar mace ko ba dan komai ba, amma dan su sami zuri'a mai kyau.

Kamar yadda muka fara da labarin wani matashi da ya bukaci a sakaya sunansa a yayin da muka tambaye shi "tsakanin farar mace da baka wacce ya fi ra'ayi?". duk da shike wannan matashi baki ne wulik! ya bayyana mana cewa ya garace ya cigaba da zama gwauro idan har bai sami farar budurwar da zata aure shi ba.

A kan haka ne muka tuntubi wasu matasa domin jin ra'ayoyinsu game da wannan maudu'i sai gashi mun yi kacibus da dama da suka tabbatar mana da cewa lallai wannan lamari haka yake, har ma wasu daga ciki suka bayyana mana cewa suna da wani sabon salo da suke cewa "Sai farar mace koda mayya ce". wato tsakanin su da bakar mace sun yi hannun riga.

Abin tambaya a nan shine, maganar da ake cewa so makaho ne ta zama gaskiya kenan?

ku cigaba da kasancewa da mu a shafukanmu na yanar gizo masu adireshi www.dandalinvoa.com da kuma voahausafacebook domin bayyana ra'ayi da kuma bada shawarwari domin anfanin matasa.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG