Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam Ya Tashi a Yankin Madagali


Sojojin Najeriya a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno
Sojojin Najeriya a bayan da suka fatattaki 'yan Boko Haram daga wani sansaninsu dake dajin Sambisa a Jihar Borno

Bayanai daga yankin Madagali na jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani bam da aka dasa a bakin hanya ya yi sanadin mutuwar wani yaro.

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa an samu tashin bam a wani yanki na karamar hukumar Madagali a yau ranar murnar sabuwar shekara.

Bayanai sun yi nuni da cewa bam din ya tashi ne a gefen hanya yayin da wasu mata da yara za su shige zuwa neman itace.

Shugaban karamar hukumar ta Madagali Yusuf Muhammad ya tabbatarwa da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz da aukuwar tashin bam din.

“Mata za su tafi neman itace da safe, sai wani yaro ya ga wani abu a rufe, ka san halin yara, sai ya dauka sai abin din ya tashi ya kashe shi.” Inji Muhammad.

Ya kuma kara da cewa mutane uku sun ji rauni da suka da wasu mata da kuma wani limamin coci guda.

“Wannan wuri ne da ba wanda zai yi tsammanin za a sa bam, wuri ne da mutane ke tafiya ko gona ko kuma wani kauye da aka kone a kwanakin baya.” Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa.

“Muna kira ga al’umarmu da su rika sa ido a kullum, duk inda ka ga abu kada ka dauka, ka je ka fada wa jami’an tsaro.” Ya kara da cewa.

Yankin na Madagali da ke arewa maso gabashin Najeriya ya sha fama da hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram inda aka tafka asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.

Saurari cikakkiyar hirar shugaban karamar hukumar Madagali da wakilinmu Ibrahim Abdulaziz:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG