Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Afirka ta Kudu Sun Cafke Mutane 300


 'Yan kabilar Zulu yayinda suke kai hari kan 'yan kasashen waje a Afirka ta Kudu
'Yan kabilar Zulu yayinda suke kai hari kan 'yan kasashen waje a Afirka ta Kudu

Gwamnati Afirka ta Kudu ta kama mutane 300 saboda wai suna da alaka da hare-haren da aka kai kan 'yan kasashen waje dake zama a kasar.

Jami’an kasar Afirka ta Kudu sunce mutane sama da 300 aka kame dake da alaka da hare haren da ake kaiwa baki ‘yan kasashen ketare har aka kashe mutane shida.

Da yake magana a taron manema labarai jiya Lahadi, ministan harkokin cikin gida Malusi Gigaba, yace “an kame masu cin zarafin bakin, kuma za’a tuhumesu da yanke musu hukunci.” Yakuma kara da cewa gwamnati tana aiki da kungiyoyin ‘yan kasashen waje domin tabbatar da taimako ga duk mutanen da wannan rigimar ta rabasu da muhallansu.

Ministan ya kara da cewa, kai hari kan duk wani ‘dan Adam da kuma lalata kaya, har ma da sata duk laifi ne, kuma baza a kyale duk wanda ya aikata hakan ba.

A jiya ne dai Shugaban Afirka ta kudu ya soke ziyarar zuwa kasar Indonisiya, domin magance wannan tashin hankalin.

Ya kuma yi magana a sansanin ‘yan ci rani daga kasashenAfirka dake kusa da birnin Durban, yana cewa duk wadanda suke son komawa kasarsu, su sani cewa zasu iya dawowa Afirka ta Kudu a koda yaushe.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG