Kungiyar Al-Shabab ta ‘dauki alhakin harin bom ‘din jiya Talata da harin da aka kai kan wani ginin gwamnati dake birnin Mogadishu.
Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Samaliya, Mohammed Yusuf ya fadawa sashen Somaliya na Muryar Amurka, cewa mutane 18 aka kashe a kalla mutane 15 ne suka raunata, a dalilin harin da aka kai kan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta kasar.
Wani shedar yace, maharan sun tada bom da suka boye cikin wata mota kusa da katangar ginin ma’aikatar ilimin, domin bai wa maharan damar shiga cikin ginin da fara harbe harbe.
‘yan bindigar dai sun sami nasarar mamaye hawa biyu a cikin ginin, amma jami’an tsaro da sojojin hadin gwiwa na Afirka, sun sami damar korar maharan bayan an yi musayar wuta.
Jami’an Somaliya sunce masu farar hula takwas ne suka rasa rayukansu a dalilin harin,tare da maharan bakwai, da jami’an tsaron kasar biyu da sojan tarayyar Afirka ‘daya duk sun rasa rayukansu.