Akasin haka, a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar mutane dubu daya da dari takwas da hamsin da biyar ne suka rasa nasu rayukkan.
Galibin ‘yan gudun hijiran dake wannan tafiyar mai cike da hadari sun fito ne daga Najeriya da Gambiya yayin da galibin wadanda suke fitowa daga Syria da Afghanistan da kuma Iraq ke ci gaba da ketawa ta Turkiya da Girka bisa ga cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin makon da ya gabata kawai, an yi kiyasin cewa, kimanin ‘yan gudun hijira dari takwas da tamanin suka mutu yayinda suke kokarin ketara tekum Baharum. Kungiyoyin jinkai sun fitar da hotunan wani ma’aikacin ceton rayuka da kasar Jamus, yana rike da gawar wani jinjiri da ya nutse, da nufin jan hankalin hukumomin kasashen turai su dauki mataki.