A yau Alhamis, jami’an Amurka sun bayyana cewar zai yi wuya a samu sauran mai rai bayan da wani karamin jirgin saman fasinja dauke da mutane 64 yayi karo da wani shelkwaftan soja a sarari samaniya tare da rikitowa cikin ruwan kogin Potomac na birnin Washington da ya fara kankarewa.
“Yanzu mun kai gabar da zamu sauya aikinmu daga na ceto zuwa na laluben gawawwaki,” kamar yadda shugaban hukumar kashe gobarar birnin Washington John Donnelly ya shaidawa taron manema labarai a filin jirgin saman Reagan National Airport.
“A wannan gabar bama zaton za’a samu wani da sauran rai,” a cewar Donnelly, inda ya kara da cewar an lalubo gawawwaki 28-ciki harda guda daga jirgin shelkwaftan.
Yayin da alfijir ya keto a wurin da hatsarin ya afku, ana iya hango jiragen ruwan agajin gaggawa dauke da fitilu masu karfi da balam-balam din da aka cika da iska da tawagar masu ninkaya suna kai kawo a wani faffadan yanki na kogin.
Donnelly ya kara da cewar ma’aikatan ba da agaji 300 ke cikin aikin ceton-da aka gudanar da galibinsa cikin tsananin duhu da sanyi.
Dandalin Mu Tattauna