Taron zai tattauna ne domin cimma manufa daya dangen da batun yada akidar zaman lafiya da kuma kyautata zamantakewa tsakanin mabiya dariku daban daban na addinin Muslunci domin kaucewa duk wasu rigingimu da ka iya tasowa a jamhuriyar Niger masu nasaba da addini.
Taron shi ne irinsa na farko da wata hukuma ta tattaro malaman dariku daban daban na adinin Musulunci kana kuma zama ne mai mahimmanci idan aka yi la'akari da kasar Niger ke ciki wadda kasashe masu fama da rigingimun kala kala suke kewaye da ita. Wani zibin ma wasu rigingimun da makwaftanta ke fama dasu suna da nasaba da addini.
Malam Samad Yahaya daraktan harkokin addini a ma'aikatar cikin gida ta jamhuriyar Niger yace taron zai kawo tasiri babba dangene da kwanciyar hankali da zaman lafiya a Niger saboda ana samun jayayya tsakanin malaman da suka fito daga makarantu daban daban. Suna anfani da wa'azinsu suna zage zagen juna. Wanna taron zai taimakesu su gane ina suka samu banbanci su kuma samu fahimta.
Taron ana iya cewa rigakafi ne domin kawo yanzu babu wata matsala da ta taso tsakanin darikun. Malam Ahmadu Abdu na hukumar USAID reshen jamhuriyar Niger yace taron yana son ya jawo hankalin darikun ne su yi la'akari da abubuwan da rashin zaman lafiya ka haifar kamar yadda ya faru a Libya da ma Najeriya.
Mahalarta taron sun ce dukansu suna bautawa Allah daya ne kuma Manzo daya ne. Suna azumi. Suna zuwa hajji da wasu aikin ibada domin haka babu wani dalilin tayar da kayar baya. Sun ce duk dan Niger mai hankali da wayo yana son zaman lafiya domin idan babu zaman lafiya ba za'a iya karantarwa ba ko a yi aikin ibada.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.