Bashir Ahmad, daya daga cikin hadiman tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a gwamnatin da ta shude, ya ce maganganun da mawakin siyasa Dauda Kahuta Rarara ya yi kan Buhari babu hikima da hankali a cikinsu.
A ranar Alhamis Rarara ya gudanar da wani taron manema labarai inda ya yi zargin cewa sai da Buhari ya lalata kasar nan kafin ya mika ta ga gwamnati mai ci.
“Sun kasa fito wa su fada wa mutane gaskiya, Buhari sai da ya kashe kasar nan ya sake ta. Sai da ya yi dama-dama da kasar nan.” In ji Rarara.
Rarara ya kuma zargi gwamnatin ta Buhari da nuna gazawa wajen magance matsalolin tsaron kasar, kazalika ya yi ikirarin cewa irin gudunmawar da ya bayar wajen kafa gwamnatin Buhari, ko shi kansa Buharin bai bayar ba.
Haka kuma mawakin ya yi korafi kan rashin ba sa mukamin minista a gwamnatin Tinubu.
Sai dai yayin da yake mayar masa da martani ta kafar Facebook Ahmad ya ce babu hankali a tattare da maganganun na Rarara.
“To a gaskiya wanda maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a ba shi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne, domin kuwa wadannan maganganun na sa sun saba da kowane irin hankali da tunani, idan dai ba akwai rashin lafiya ba, to lalle akwai tsantsar jahilci. Babu hikima a cikin maganganun nasa ko kadan.
“Na farko, cikin videon, Rarara ya yi ikirarin cewa wai gudunmawar da ya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai bawa kansa irin wannnan gudunmawa ba. IKON ALLAH. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?
“Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a ba shi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a bawa mukaman na ministoci. TASHIN HANKALI. Ko akwai chemistry, balle technology a cikin wannan batu?” In ji Ahmad.
Ahmad ya kara da cewa “a kuma maganar da Rararan ya yi da cewa wai a cikin shekaru bakwai na Baba Buhari ba a iya bin hanyar Abuja zuwa Kaduna, a zahirin gaskiya ba zan ce ba a samu matsalolin tsaro a hanyar ba, sai dai zan dan yi masa tuni da ya tuna baya a lokacin da Baba Buharin ya karbi mulki, ba ma maganar kidnapping ake yi a hanyar ba, Saboda matsalar da Boko Haram ta jefa yankin Arewa daga Abuja zuwa Kaduna sai an ci karo da shingen jami’an tsaro sama da goma, ba ma maganar daga Kaduna zuwa Kano ba, balle uwa uba, daga Kano zuwa Maiduguri. Duk wanda yake da hankali zai godewa Allah akan wannan.”
Rarara ya yi ikirarin cewa "duk wani kulle-kulle da aka yi don Tinubu ya fadi, na sani, kuma 'yan APC ne, wasu ma suna nan a akan mukamai."
Kalaman da Rarara ya yi na zuwa jim kadan bayan da kotun kolin Najeriya ta kara jaddadawa Shugaba Tinubu nasarar da ya samu a zaben 2023.
Kotun dai ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour party suka daukaka.
Maganganun Rararar har ila yau sun ta da kura a kafafen sada zumunta inda jama’a da dama suka yi ta tsokaci akai.
Shi dai Rarara shi ne ya rera wa Buhari wakar “Masu Gudu Su Gudu,” shi ne kuma ya rera wakar “Jagaba,” da “Jagaba Ya Karbi Kasa.”
Dandalin Mu Tattauna