Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar da Sabon Sarkin Agae a Jihar Neja


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Alhaji Yusuf Nuhu ya zama sabon sarkin Agae biyo bayan rantsar da shi

A shekarar da ta gabata ne aka zabi Alhaji Yusuf Nuhu a matsayin sarkin garin Agae na goma sha uku lokacin da masu zaben sarkin masarautar suka zabeshi.

An zabeshi ne bayan mutuwar tshohon sarkin garin Alhaji Muhammad Kudu na uku. Yayin da yake jawabi gwamnan jihar Neja Dr Muazu Babangida Aliyu ya tabo maganar babban zaben kasa da za'a yi watan gobe.Yace sarakunan gargajiya suna da rawar da zasu taka na tabbatar da cewa an gudanar da zabukan da za'a yi cikin zaman lafiya da lumana.

Shi ma sabon sarkin a cikin jawabinsa ya mayar da hankali ne kan batun zaben mai zuwa. Yace yayi anfani da zarafin da ya samu ya kira 'yan siyasa da magoya bayansu da su ji tsoron Allah su bi dokokin kasa domin tabbatar da ganin an yi zaben cikin adalci ta yadda zai zama karbabbe.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG