Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babangida Aliyu Ya Sha Da Kyar


Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja
Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Tsohon Gwamnan Jahar Naija, Babangida Aliyu, ya sha da kyar bayan da matasa suka far mai a wajen taron mika mulki ga sabuwar gwamnatin jahar.

Wakilin Muryar Amurka ya ruwaito cewa wasu matasa ne su ka yiwa tsohon gwaman ruwan duwatsu bayan da aka kusa kammala taron.

Bayanan da wakilinmu ya aiko sun nuna cewa sai da jami’an tsaro suka yi ta harbi a sama domin tsorata matasan kafin a samu a fice da shi daga filin taron.

Har ila yau sai da jami’an tsaron suka harba borkonon tsohuwa kafin baya ga harba bindiga kafin a samu a tsiratar da tsohon gwamnan.

A jiya Juma’a aka rantsar da sabbin gwamnatoci a matakin tarayyar da jahohi a Najeriya.

Tsohon gwamna Babangida Aliyu, ya sha kayi a takarar neman sanata a jahar ta Naija, kana dan takararsa na gwamna a jam’iyyar PDP ya sha kayi, lamarin da ya baiwa APC damar karbe mulkin Jahar.

Gabanin aukuwar hakan, sabon gwamnan jahar ta Naija, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce akwai dumbin matsaloli da ya gada a jahar da kuma tarin bashi, amma ya ce duk da haka zai yi iya bakin kokarinsa.

Domin jin tsokacin da tsohon gwamnan jahar Kano, Kanar Aminu Isa Kwantagora ya yi game da jifan Babangida Aliyu da aka yi latsa wannan sauti:

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG