Bayan mako guda da wallafa bayanin karbar mukami a shafinsa na X wato Twitter da tsohon kakakin kungiyar Dattawan Arewa wato Northern Elders' Forum, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya yi, kungiyar ta sake jaddada cewa ba wakilcinta ya kai dakta karbar mukami a ofishin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ba.
Kungiyar ta ce ya je ne a bisa kashin kansa lamarin da masana siyasa suka ce ba sabon abu ba ne.
A rana Litinin 18 ga watan Satumbar da muke cikin ne tsohon daraktan harkokin yada labaran kungiyar Dattawan Arewan ya sanar da ‘yan Najeriya a shafinsa na X cewa lokaci ya yi da zai fito ya fada wa al’umma cewa ya karbi mukamin mai baiwa mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima shawara a kan siyasa lamarin da ya jawo kalmomin suka masu karfi inda wasu kalilan suka masa fatan alkhairi.
Tuni dai kungiyar dattijan ta nesanta kanta da mukamin da aka bai wa Baba-Ahmed ta bakin daraktan gudanarwar ta, Alh. Nastura Ashir Sharrif.
A cewar Nastura kungiyar ta sa kai ce, kuma ba wakilcin kungiyar ne tsohon daraktan harkokin yada labaransu ya je yi ba illa zuwa can a bisa kashin kansa.
A wani bangare kuwa, masani a kan sha’anin siyasa, tattalin arziki kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mal. Baba Yusuf, ya ce karban mukamin da dakta Hakeem Baba-Ahmed ya yi ba wani sabon abu bane kasancewar sa dan kasa kundin tsarin mulki ya bashi damar ya karbi mukami.
Karban mukamin dakta Baba-Ahmed dai na ci gaba da janyo muhawara mai karfi a kafofin yanar gizo inda 'yan Najeriya daga sassan kasar daban-daban ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.
Idan Ana iya tunawa, a watan Febrairun shekarar 2017 ne shugaban Majalisar Dattawa ta 9, Sanata Bukola Saraki ya nada Dr. Hakeem Baba Ahmed a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadarsa a wancan lokacin.
Kazalika, Dakta Baba Ahmed mai shekaru sama da 65 a duniya ya yi karatun digirinsa na farko ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma ya kasance babban sakatare a lokuta daban-daban a fadar shugaban kasa sannan daga baya ya koma ma'aikatar kasuwanci da masana’antu da dai sauransu.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna