Takaddamar da ta kaure tsakanin Najeriya da kamfanin Twitter na ci gaba da kara rincabewa yayin da kamfanonin sadarwa a kasar suka bi umarnin da gwamnatin tarayya ta ba su, na su rufe ayyukan Twitter a kasar.
Kafafen yada labaran Najeriya da dama sun ruwaito cewa kungiyar kamfanonin sadarwa ta ALTON ta rufe hanyoyin shiga shafin na Twitter.
Kamfanin NOI da ke kiddiga kan kafafen sada zumunta, ya ce mutum miliyan 39 ne ke amfani da Twitter a Najeriya,
Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun shugabanta Engineer Gbenga Adebayo da babban sakatarenta, Gbolahan Awonuga, kungiyar ta sanar da daukan wannan mataki.
“Bisa ga dokar Najeriya da ta shafi fannin sadarwa ta 2003, wacce ke kare muradin kasa, wacce kuma a karkashinta lasisin kamfanonin ke aiki; mambobinmu sun bi umurnin da hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta NCC ta bayar.” Sanarwa ALTON ta ce kamar yadda kafafen labarai suka wallafa.
Bincike ya kuma nuna cewa, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ita ma ta bi sahu, inda har ta kai ga rufe shafin nata baki daya, wanda ke da mutum akalla miliyan da suke bi.
A ranar Juma’a hukumomin Najeriya suka bayyana matakin haramta shafin a kasar, inda suka yi kira ga kamfanonin sadarwa da su rufe kafar sada zumuntar ta Twitter.
Wannan rikici ya samo asali ne bayan da kamfanin Twitter ya goge wani sakon da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa a ranar Laraba.
Sakon ya yi gargadi ne ga kungiyar IPOB da ake zargi da ta da kayar baya a kudu maso gabashin Najeriyar, inda ya yi masu nuni da irin asarar rayukan da aka yi a yakin basasan da Najeriya.
A cikin sakon, Buhari ya yi ikirarin cewa, gwamnatin Najeriya, za ta tafiyar da masu kai hare-hare a yankin da daidai da abin da ya kamace su, kalaman da wasu ke nuni da cewa, barazana ce ga mazauna yankin, wanda ya yi yakin Biafra, abinda ya sa aka yi asarar rayukan ‘yan Najeriya da dama.
Twitter ya yi maza ya goge sakon Buharin, wanda ya ce ya saba ka’idojin kamfamin.
Bisa ka’ida, kamfanin na Twitter ba ya yarda a wallafa wani sako da zai iya ta da hankali ko barazana ga wani ko wasu.
Wannan mataki bai yi wa Najeriya dadi ba, inda ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna goyon baya ga kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, wacce hukumomin kasar suka haramta.
A cewar Mohammed, ‘ya’yan kungiyar ta IPOB na wallafa bayanai da suka fi na Buhari muni, amma duk da haka Twitter bai dauki mataki akai ba.
"Ana yawan amfani da shafin wajen gudanar da wasu ayyukan da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya.” wata sanarwa da mataimakin na musamman ga Lai Mohammed, Segun Adeyemi ta ce.
“Kungiyar da take ba mambobinta umarnin su kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda, su kashe ‘yan sanda, su kai hari gidan yari, su kashe gandurobobi, sai kuma a ce shugaban kasa ba shi da ikon ya nuna fushinsa? Mohamed ya fadawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba, kamar yadda kafafen yada labaran kasar da dama suka ruwaito.