Atoni Janar na Amurka William Barr ya ce sakon Twitter da shugaba Donald Trump ya wallafa akan ma’aikatar shari’a da ma’aikatanta da kuma ayyukan su yana sa ya zama da matukar wahala ya gudanar da aikinsa.
Wannan sanarwa ta zo da mamaki daga daya daga cikin na hannun daman shugaba kasa da ta fito jiya Alhamis, kwanakin kadan bayan ma’aikatar shari’a da Barr ya ke shugabanta ta canja shawarar da masu gabatar da kara na ma’aikatar suka bayar.
Inda suka kuma bada shawarar hukunci mai sauki da za’a yankewa dadadden na hannun daman Shugaba Trump, Roger Stone, da aka yanke masa hukunci na yiwa majalisa karya da hana shari’a aiki da kuma yin katsalandan ga shaidu a binciken Rasha na yin katsalandan a zaben Amurka.
Shugaba Trump ya yi korafin cewa shawarar yanke hukuncin shekaru 7 zuwa 9 na “Abin takaici ne” kuma “Babu adalci.” Ba kasafai ake ganin ma’aiaktar shari’ar Amurka ta canja shawarar da lauyoyinta suka bayar ba a shari’ar mai laifi.
Masu gabatar da kara guda hudu a shari’ar Stone sun janye daga shari’ar, a ciki har da mutum daya da ya ajiye aikisa daga ma’aikatar shari’ar.
Za’a yankewa Stone hukunci a mako mai zuwa. Shekaru 7 zuwa 9 da masu gabatar da kara suka bada shawara yi ya yi daidai da tsarin yanke hukunci na tarayya saboda irin wadannan laifuka, amma ya rage ga ita alkaliyar, Amy Berman Jackson, ta yanke hukunci na iya tsawon lokacin da za’a kulle shi.
Facebook Forum