Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Archbishop Desmond Tutu Na Afirka ta Kudu Ya Rasu


Archbishop Desmond Tutu
Archbishop Desmond Tutu

Mai fafutukar yaki da mulkin wariyar launin fata na Afirka ta Kudu, Archbishop Desmond Tutu, ya mutu yana da shekara 90. 

Tutu wanda ya taba samun lambar yabon zaman lafiyar Nobel Peace Prize ya yi fice a fadin duniya saboda gwagwarmayar da ya yi ta yaki da wariyar launin fata, gwarzo kuma wajen kare hakkokin bil’adama.

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ne ya sanar da mutuwar ranar Lahadi.

“Mutuwar Archbishop Desmond Tutu ta bude wani babi na alhini da jimami a kasarmu yayin da muke wa fitattun ‘yan Afrika ta kudu da suka yi yakin samar wa kasar ‘yanci bankwana,” a cewar shugaban.

Tutu ya wuce matsayin jagoran addini nesa ba kusa ba.

Ya shafe tsawon rayuwarsa yana fafutukar kare hakkin bil’adama, da caccakar rashin adalci, cin hanci da rashawa da kuma tauye hakkoki.

Tutu ya taba samun lambar yabon zaman lafiya ta Nobel Peace Prize a shekarar 1984 saboda gwagwarmayar da ya yi ta adawa da mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu.

A lokacin da aka saki marigayi Nelson Mandela daga kurkuku, gidan Tutu ya fara sauka ranar farko bayan an ‘yantar da shi.

Daga nan Archbishop Tutu ya gabatar da Mandela ga jama’a a matsayin shugaban kasa bakar fata na farko a Afrika ta kudu a shekarar 1994.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG